Buhari ya baiwa Afghanistan kyautar Dala miliyan 1 a tallafawa gajiyayyu da talakawa a kasar
Ƙungiyar Haɗin kan Musulmi, OIC, ta yaba wa Gwamnatin Taraiya bisa gagarumar kyautar da ta baiwa Gidauniyar Tallafin Jinƙai ta Afghanistan.
Sakatare-Janar na OIC ɗin, Hissein Brahim Taha ne ya yi yabon a wata sanarwa da shelkwatar ƙungiyar ta aike wa jaridar Daily Nigerian a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce tallafin ya zo a daidai lokaci domin kungiyar ta samu damar ƙara aiyukan jin kai da a ke yi a Afghanistan.
- Advertisement -
Sanarwar ta ƙara da cewa Tallafin kuɗin zai taimaka a tallafa wa miliyoyin mutane maza da mata da ƙananan yara a Afghanistan.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a watan Disamba 2021 ne OIC ta kaddamar da Gidauniyar tallafin domin magance wahalar da al’umma su ke sha a Afghanistan a wani babban taro da ta haɗa.
Haka zalika Nijeriya ita ma mamba ce ta OIC din kuma na ɗaya da ga cikin ƙasashen da suka sanar da tallafin.