Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Za Ta Mikawa Amurka DCP Abba...

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Za Ta Mikawa Amurka DCP Abba Kyari

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta amince da bukatar Amurka, na a mika mata dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, bisa alakarsa da shahararren dan damfara Abass Ramon aka Hushpuppi da wasu mutum hudu.

Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana hakan a karar da ya shigar gaban shugaban Alkalan babban kotun tarayya dake Abuja kan lamarin, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022 karkashin dokar Extradition Act.

- Advertisement -

Wannan kara da ya shigar ya biyo bayan bukatar Abba Kyari da wakilin jakadan Amurka yayi a Abuja.

Antoni Janar ya bayyana cewa lallai ya gamsu da cewa zargin da ake yiwa Abba Kyari ba tada alaka da siyasa kuma babban laifi ne.

Yace: “Idan aka mikashi ga Amurka, ba za’ayi masa rashin adalci ba, ba za’a azabtar da shi ba, ba za’a hanashi yancinsa ba saboda launin fatar jikinsa, asalinsa ko siyasarsa ba.”

Ya kara da cewa dubi ga laifukan da ake zarginsa da su, ba za’a ce an yi masa rashin adalci ba idan aka mika shi.

Masu karatu shin ko kuna goyon bayan hakan?

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: