Hukumar sufurin jiragen kasa ta dakatar da zirga-zirgan jirgin Kaduna zuwa Abuja sakamakon harin yan bindiga
Daga Muryoyi
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC ta dakatar da zirga-zirgar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja har sai yadda hali yayi.
Wannan dai na faruwa ne bayan da wasu yan ta’adda suka kai hari kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna da misalin karfe 8 na daren ranar Litinin a daidai Katari
- Advertisement -
Muryoyi ta ruwaito mutane da dama sun mutu a harin sannan an raunata wadansu kana kuma masu garkuwan sun kwashi mutane da dama. Muryoyi ta ruwaito akwai jiga-jigan mutane a ciki wanda ya hada har da tsohon mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Wakala da tsohon Kwamishinan jihar Kaduna da DG na KADFAMA da sauransu.