DA DUMI-DUMI: Masu garkuwa sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna dauke da fasinjoji 970
DA DUMI-DUMI: Masu garkuwa sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna dauke da fasinjoji 970
Daga Muryoyi
Wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kai farmaki a jirgin kasan Abuna zuwa Kaduna na yammacin yau (karfe 6) inda suke ta harbe-harbe bayan sun tsaida jirgin cak
Har karfe 9 na daren nan Muryoyi ta jiyo cewa masu garkuwan na cin karensu ba babbaka a jirgin.
- Advertisement -
Rahotanni sun nuna masu garkuwam sun kai harin ne a tsakanin Katari da Rijana akalla minti 20 zuwa Kaduna.
Masu garkuwa sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kadunan ne wanda ke dauke da fasinjoji akalla 970