Da Dumi-Dumi: Mutumin da ya jagoranci kamfen din El-Rufai yaci Gwamna a 2019 Ben Kure ya fice daga APC zuwa NNPP
Mutumin da ya jagoranci kamfen din El-Rufai yaci Gwamna a 2019 Ben Kure ya fice daga APC zuwa NNPP
Daga Muryoyi
Babban Daraktan yakin neman zaben El-Rufai a 2019 Honourable Ben Kure ya sauya sheka daga APC zuwa NNPP,
Muryoyi ta ruwaito Mista Ben Kure ya rubutawa APC takardar cewa ficewa daga jam’iyyar tun a ranar 1 ga watan Maris din 2022 amma bai bayyana dalili ba.
- Advertisement -
Mista Ben dai shine ya jagorancin kawo El-Rufai ya zama Gwamna a 2015 da kuma a 2019
Tuni dai Mista Ben ya ajiye duka mukaman da yake rike dasu a APC da Gwamnatin jihar Kaduna duk da cewa Mista Ben na cikin iyayen jam’iyyar APC da suka kafa ta a Kaduna