Magidanci ya sayar da ‘ya’yan makwafcinsa 6 da sunan kaisu makaranta 

Daga Zainab Adamawa Jaridar Taswira

WAKILANMU daga Jihar Adamawa sun ce, a tsakiyar makon nan ne wata Kotun Majistare a birnin Yola, ta tasa keyar wani mutum Mai suna, Yohanna Saidolo, bisa zargin satar ‘ya’yan makwabcinsa har guda shida, ya sayar da su, da sunan wai ya kai su wata makarantar Mishan.

Tun da fari dai, Mai Gabatar da karar Sufeto Ibrahim Aliyu, ya sanar da Kotun cewa, wani mazaunin kauyen Koma, Mai suna, Markus Anthony, da wadansu mutane biyar ne suka kai rahoto gun hukumar ‘yan sanda a ranar 5 ga Fabrairun wannan shekarar. Inda suka nuna cewar Mista Saidolo ya yaudare su, inda ya kwashi yara har guda shida, ya kai su wani waje da babu wanda ya sani.

Jaridar WAKILIYA ta ruwaito cewa Mista Anthony, ya sanar wa hukuma yadda abin ya faru, inda ya ce, tun da fari, wanda ake zargin ya shaida mu su cewar zai yi wa yaran rajista ne a wata makarantar Majami’a ta Mishan, a cikin garin Jimeta, amma daga bisani, lamarin ya zama na banza. Domin, a cewar Mista Anthony, maimakon a sami labarin yara na ci gaba da karatu a makaranta, sai aka nemi labarinsu, ba a samu ba.

- Advertisement -

Bayan gabatar da karar, Mai Shari’ah, Alheri ya bayyana cewa, laifin ya ci karo da shashi na 257 da 259 na tsarin dokokin kasa, wadanda aka sake tabbatarwa a shekarar 2018.

Alkalin, daga bisani, ya dage sauraren karar zuwa ranar 25 ga Maris, 2022, domin ba wa hukumar bincike su gudunar da dukkanin shirye-shirye da bincike, kamar yadda suka nema, tare da tasa keyar wanda ake zargin zuwa gidan maza.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: