Mata a Saudiyya sun koma yin sana’ar taxi gadan-gadan saboda tsadar rayuwa

Daga Muryoyi

Rahotanni a baya-bayan nan na nuna cewa mata a kasar Saudiyya na yin kabo-kabo da motoci wato tazi domin samun karin kudaden shiga don rufawa kansu asiri sakamakon tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta

Sai dai galibi zawarawa ne ke yin sana’ar tukin motar ko kuma matan da mazajensu sukayi ritaya

Muryoyi ta ruwaito wata mata, Fahda Fahd yar shekara 54 mai ‘yaya Uku ta ce tana sana’ar daukar fasinjoji da motar ta ne domin rufawa kai asiri ganin cewa mijinta ya manyanta kuma yayi ritaya ba tare da tara dukiya ba.

- Advertisement -

Tace duk da dai ita ma’aikaciya ce a wani Asibitin Riyadh amma dai albashinta baya isa ta biya bukatun ta da na ‘iyalin ta shi yasa ta yanke shawarar hada aiki da kuma yin taxi

Fahd na samun albashi Riyal 4,000 (kwatankwacin $1,066) a wata wanda baya isarta har sai tayi aikin mota ta samu karin Riyal 2,500. Hakan na taimaka mata taya mijinta wajen biyan kudaden makarantar yara da kuma wasu kudaden haraji da sauran dawainya na yau da kullum.

Muryoyi ta ruwaito daga karshen shekarar 2021 mata a kasar Saudiyya sun tsunduma neman aiki sakamakon hauhawa da tsadar rayuwa. Kididdiga ta nuna yanzu kashi 1 bisa 3 na ma’aikata a Saudiya mata ne.

Muryoyi ta kai a yanzu mata na sana’ar sayar da mai, takalmi, kasuwanci, aiki a gidajen sayar da abinci da wajajen kantunan sayar da kaya da sauran sana’o’i wadanda a baya yan kasahen waje ke yi.

Sauran matan da aka tattauna da su masu sana’ar tuka mota sun hada da
Insaf, yar shekara 30 mai ‘yaya Uku wacce ta kama sana’ar tazi bayan rasuwar mijinta.

Tun daga 2018 da aka baiwa mata damar tuka mota a Saudiyya kawo yanzu akwai mata sama da dubu 200 dake da lasisin tuka mota a kasar.

Sai dai a kasar Saudiyya doka bata yarda mata su rika yin cudanya da baligan maza ba. Hakan ta sanya mafi yawan lokuta mata fasinjoji da kananan yara kadai mata yan tazi suke diba a matsayin fasinjoji kodayake ana samun mace ta dauki namiji amma ba kasafai ba.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: