NDLEA Ta Ƙwato Tramadol 294,440, wasu ƙwayoyi a Delta, Bauchi, Da Filin Jirgi Na Lagos

NDLEA Ta Ƙwato Tramadol 294,440, wasu ƙwayoyi a Delta, Bauchi, Da Filin Jirgi Na Lago

….An kama mutane 41 da ake zargi a wani samame a Kaduna, Abuja; ta kama gidan harsashi 38,862 a Anambra

Daga Mahmud Isa Yola Hedikwatar NDLEA, Abuja
Lahadi 6 Maris 2022

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA, sun kama ƙwayoyin Tramadol, Diazepam, Swinol, Rohyphnol da Exol-5 a kalla 294,440 tare da wasu miyagun ƙwayoyi a manyan sumame a jihohin Delta, Bauchi, da filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) a birnin Ikko, Legas, yayin da aka kama mutane 41 da ake zargi biyo bayan samame da hukumar tayi a Abuja da jihar Kaduna.

- Advertisement -

A jihar Delta, an kama Christian Onah, mai shekaru 42, a mahadar Isele-Azagba tare da ƙwsyoyin Swinol guda 23,160 da kuma Rohypnol guda 66,000, wadanda nauyinsu ya kai kilogiram 71.6 yayin da suke safarar su daga Benin, Edo zuwa Onitsha, jihar Anambra. A wani kamun kuma, an kama wata motar kasuwanci daga Onitsha zuwa Ibadan, jihar Oyo a mahadar Abraka, Asaba a ranar Laraba 2 ga watan Maris dauke da kafso-kafso na Tramadol 78,000; ƙwayoyin Diazepam 5,000 da Exol-5 guda 97,500 , yayin da aka kama wanda ake zargi, Olaniyan Sunday, mai shekaru 42. Akalla, an kama wata mata da ake zargi mai suna Patricia Saduwa, ‘yar shekara 42 da tabar wiwi kilogiram 233.7 a wani samame da aka kai a yankin Orogun da ke kusa da garin Abbi a karamar hukumar Kwale, jihar Delta a ranar Juma’a 4 ga watan Maris. Sumame da aka kai wani gida a unguwar a ranar ya kai ga kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 123.7 yayin da mai shi ya tsere.

A Bauchi, jami’ai ma su aiki da bayanan sirri sun kai samame a wani dakin ajiyar kaya dake Gadar-Maiwa, a karamar hukumar Ningi a jihar, inda aka yi nasarar ƙwato 542.5kg na tabar wiwi; ƙwayoyi 6,800 na Diazepam, ƙwayoyi 12,400 na Exol-5 a ranar Laraba 2 ga Maris.

Akalla mutane 30 ne aka kama a unguwar Malali da ke cikin garin Kaduna a wani samame da aka kai da nufin lalata wuraren hada miyagun ƙwayoyi a fadin jihar. A ranar Alhamis 3 ga watan Maris ne aka kama wani da ake zargi Usman Dahiru da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 24 a boye a cikin buhu biyu na wasu kaya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda nan ne kuma aka kama wani da ake zargi mai suna Abdulrazaq Rabi’u da kudin jabun dalar Amurka 100,000 a ranar.

Jami’an tsaro a jihar Anambra sun kwato gidan harsashi guda 38,862 tare da kwali 13 na haramtattun kwayoyi a lokacin da suka kai samame a wani dakin ajiyar kaya dake Onitsha. A Abuja, babban birnin tarayya, an kama mutane 11 da ake zargi da kuma 81.2kg na kwayoyi a wani samame da aka kai a ranar Asabar 5 ga watan Maris a maɓuyar masu laifi da suka haɗa da Torabora, mayankan Karu, tashar motocin Jabi da kuma forest.

A filin jirgin saman Legas, an kama wani Audu Muhammed a sashin kamfanin safarar kaya na SAHCO a ranar Asabar 5 ga watan Maris da tabar wiwi kilogiram 1.550 a boye a cikin buhunan abinci na golden morn da aka yi niyyar zuwa Dubai, UAE da su. Kwanaki biyu gabanin ranar, wato Alhamis 3 ga watan Maris, an kuma kama wani da ake zargi, Olalekan Wasiu Ayinde dauke da kafso-kafso na Tramadol guda 4,980; kafso 600 na Rohypnol da wasu magunguna na zanen da aka ɓoye a cikin kayan abinci don fitarwa zuwa ƙasar Afrika ta kudu.

A ɗaya ɓangaren kuma, babban wanda ake zargi da shigo da ƙwayoyin Captagon guda 451,807 masu nauyin kilogiram 79.119 a watan Satumba, 2021 a tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke Legas, Nwoku Princewill Uche, mai shekaru 36, ya shiga hannu bayan watanni shida yana gudu. Ƙwayoyin wadanda suka shahara da sunan maganin ƙarfin Jihadi, sune karo na farko da aka kama irin su a Yankin Yamma da Tsakiyar Afirka. A cikin bayanansa, ya yi ikirarin cewa ya gana da wanda ya ba shi aikin a LinkedIn yayin da aka biya shi Naira Miliyan biyar ya biya kudin kwantena. Daga nan sai ya yi amfani da asusun banki na ɓangare na uku don samun takadda mai taken Form M don share fage ga haramtattun kayayyakin.

Yayin da yake yabawa jami’an hukumar NDLEA na Delta, Bauchi, Kaduna, Anambra, Abuja, tashar jiragen ruwa da kwamandojin MMIA bisa kame da ƙwato muggan ƙwayoyin, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya buƙacs su da sauran ‘yan uwansu dake faɗin ƙasar nan da su ci gaba da zama a ankare tare da kai farmaki har sai an wargaza duk wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: