RIKICIN RASHA: Kowa yayi tanadi, za’a fuskanci masifar karancin abinci a Najeriya nan da watan Yuni -Inji Dangote
Daga Muryoyi
Kowane dan Nijeriya yayi tanadi, domin za ayi karancin abinci mai tsanani nan da watanni biyu masu zuwa a kasar nan, cewar Dangote
Attajirin dan kasuwa kana Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya gargadi yan Najeriya cewa kowa yayi tanadi kuma a kwana shirin tsindumawa cikin matsanancin karancin abinci da tsananin yunwa a kasarnan nan da watanni biyu masu zuwa saboda rikicin Rasha da Ukraine dake cigana da munana a yanzu haka.
Dangote a don haka sai ya shawarci Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta dakatar da kasuwancin fitar da masara zuwa kasashen waje.
- Advertisement -
A hasashen Dangote daga nan zuwa watan Yuni ne tsadar zata soma a Najeriya da sauran sassan Duniya