Saudiya ta raba wa mata na’urar jin magana domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Harami
Saudiya ta raba wa mata na’urar jin magana domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Harami
Daily Nigeria ta ruwaito Babban Ofishin kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya raba na’urar jin magana 200 ga mata da ba larabawa ba domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Masallatan Haramin guda biyu.
Shafin Haramain Sharifain ya wallafa cewa an ɗauki matakin ne domin baiwa mata da ba larabawa ba damar sauraron huɗubar sallar Juma’a da fahimtar ta.
- Advertisement -