Taƙaitacciyar Wasiƙa Zuwa Ga Matasan Arewa

Taƙaitacciyar Wasiƙa Zuwa Ga Matasan Arewa

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Muna Kira ga ƴan uwan mu Matasan Arewacin Najeriya, da mu gane cewa lokaci yayi da ya kamata mu farka daga dogon Baccin da mukeyi.

Inaso nayi amfani da wannan damar, domin aika saƙo ga Matasan mu masu Albarka,

- Advertisement -

1. Abu na farko da ya kamata nayi mana tuni akai shine, Matasa mune ƙashin bayan Al’umma, Idan mun lalace tamkar Al’ummace ta lalace, ya kamata musan haka,

Mu sani lokaci Yana zuwa nan gaba kaɗan, dan haka tun yanzu ya kamata mu lura sosai, wajen gane Shuwagabannin da suke sonmu da cigaba, kada mu yadda ayi amfani damu wajen tada zaune tsaye, ko ayi amfani damu wajen aikata fasadi, Wannan Ba aikin Matashi bane.

Duk inda Matashin Arewacin Najeriya yake ansan shi da Neman halal nashi, ba wai aikin tada zaune tsaye ba, Saidai kash yanzu Abun ya sauya to Amma ba’a Makarar Gyara.

2. Ina ƙara yi mana tuni da wata magana da wani tsohon Shugaba ya faɗa akan mu na cewa wai, Matasan Arewa kamar ƴan kaji suke da zarar lokaci yayi idan muka watsa musu yan Silalla zasu biyo mu.

Yanzu lokaci yayi da zamu nuna masa cewa Hasashen sa Ba haka yake ba, Hanya mafi sauƙi itace kada mu sayar da ƴancin mu Dan wasu ƴan kuɗin da baza su amfane mu ba.

3. Akwai hanyoyin da Zamu taimaki kanmu ba tare da mun saida ƴancin mu Ba,

Ansan mu da Noma da kiwo, Sannan Allah ya albarkacemu da ƙasar Noma wanda ba abinda zamu shuka bai fito ba, Mu keda wajen kiwo a yankin mu na Arewa,

Kada muyi dogaro da karatun da mukayi wai lallai sai shine zai kawo mana Cigaba a’a ba lallai sai shi ba, Akwai hanyoyi da dama, Karatu yana da matuƙar muhimmanci a rayuwa, dan haka karmu dogara wai lallai sai munyi akin Gwamnati.

Ya kamata musan cewa zamu iya yin sana’o’i da dama wanda zasu taimakemu wajen riƙe Iyalan mu.

Ina takaici sosai idan na waiga naga duk wani aikin fasadi da matashi ake shirya shi, badan komai ake hakan ba, sai dan a samu wasu yan kuɗaɗe wanda baza su taɓa raba mu da wahala ba tunda bana halan bane.

Wannan yana ɗaya daga cikin manya manyan manufofin Ƙungiyar “Arewa Media Writers” na Bawa matasan Arewa Kariya da faɗakar dasu don kada su Shiga Ƙungiyoyin tada zaune tsaye.

Ƙungiyar”Arewa Media Writers” ƙarƙashin Jagorancin Hazikin Marubuci Comr Abba Sani Pantami tana fatan Matasan Arewa zasu cire hannun su akan duk abinda bazai haifarwa da yankin mu da ƙasar mu ɗa mai ido ba, mu rungumi zaman lafiya da juna, sannan mu rungumi sana’a, hannu bibbiyu Insha Allah za mu yi Nasara.

Allah yaƙara taimakon Matasan mu na Arewa dama yankin namu baki ɗaya.

Rubutawa✍🏻✍🏻✍🏻
Yusuf Finance,
Shugaban Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Reshen Ƙaramar Hukumar Dapchi Bursari, Dake Jihar Yobe.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: