Daga Muryoyi
Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmunini Kabir Usman ya bayyana cewa tsohon Gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu dan Katsina ne mai lasisi wanda ke da dadaddiyar dangantaka da masarauta tun fiye da shekara 30 da suka wuce.
Majiyar Muryoyi ta ruwaito Sarkin yayi wannan furucin ne a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawagar tallata takarar Tinubu da ta kai masa ziyara ranar Juma’a a masarautarsa
Sarki Abdulmuminu ya cigaba da cewa fiye da shekaru 30 da suka gabata, tsohon Gwamnan jihar Legas din ya na dan kyakkyawar alaka da masarautar tun lokacin da mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Kabir Usman ke karagar mulki don haka zai bayar da dukkan goyon bayan sa ga tafiyar siyasar ta sa.
- Advertisement -