Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuWahalar man fetur: Ƴan ga-ruwa sun tafi yajin aiki a Kano

Wahalar man fetur: Ƴan ga-ruwa sun tafi yajin aiki a Kano

Wahalar man fetur: Ƴan ga-ruwa sun tafi yajin aiki a Kano

Al’ummar unguwannin Walawai da Unguwa Uku a Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano sun wayi garin jiya da matsalar ƙarancin ruwa sakamakon yajin aikin da masu sayar da ruwa, waɗanda a ka fi sani da ƴan ga-ruwa a jihar su ka fara yi.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ƴan ga-ruwan sun tafi yajin aikin ne sakamakon wahalar man fetur da ta sanya masu gidajen ruwa sun ƙara farashin sabo da man fetur ya yi tsada.

A cewar ƴan ga-ruwan, sun kasance su na sayar da duk jarka ɗaya a kan N20, amma sabo da karin kudi da masu gidajen ruwa, inda su ke saro ruwan, su ka yi musu, shine suma su ka ƙara N10 a kan ko wacce jarka, ya zama N30 kenan.

- Advertisement -

Sai dai kuma ƴan ga-ruwan sun koka da cewa mutanen gari sun ƙi amincewa da ƙarin farashin, inda su ke matsa wa a sayar musu da jarka uku a kan N50.

“Mu kuma mu ka ga ba za mu iya sayar wa a kan N20 kowacce jarka ba, shi ya sa mu ka ce kawai mu haƙura da sayar da ruwan har sai komai ya daidaita,” in ji ƴan ga-ruwan.

“Bayan haka kuma ba za ku iya sayarwa a kan harka uku N50 ba. Gara mu zauna mu dena sayar da ruwan sabo da mun fuskanci al’umma sun ƙi yarda. Sun kasa fahimtar cewa mu ma na yi mana ƙarin N20 a kan kowacce kura,” in ji su.

Bello Na-Alla, Shugaban masu Gidajen ruwa na yankin ya ce ƴan ga-ruwan ba su yi laifi ba da su ka tafi yajin aiki sabo da al’umma basu fahimci cewa su ma an yi musu ƙarin kuɗi ba.

A cewar Na-Alla, su na sarar wa ƴan ga-ruwan ruwa a kan N80 ko wacce baro, amma sabo da tsadar da man fetur ya yi, dole an maida shi N100 a kan ko wacce baro.

Ya ƙara da cewa masu gidajen ruwa na dayan galan ɗin man fetur a kan N3,600, saɓanin a da a na sayar da shi N1,200.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su fahimci yanayin da a ke ciki, su bada haɗin kai su riƙa aiyana ruwan a kan N30 a duk jarka, inda ya ce su suke amfana da ruwan kuma dole ne a yi amfani da shi.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ƴan mata ne dai da ƙananan yara ke ta yawo da ababan ɗiban ruwa domin neman ruwan da za a yi amfani da shi a yankin.

Rahotanni ma sun baiyana cewa mutanen yankin sun fara shiga wani mawuyacin hali inda yara ba su samu zuwa makaranta ba sabo da ba ruwan da za a yi musu wanka da karin kumallon safe.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: