Yahaya Bello ya taya Obasanjo murnar cika shekara 85, ya ce “Obasanjo bawan Allah ne mai son cigaban Najeriya da Afrika

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kogi kana dan takarat neman shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC Yahaya Bello ya taya tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo murnar kara shekara a yau Asabar,

Muryoyi ta ruwaito Obasanjo ya cika shekara 85 a duniya. Yayaha Bello ya ce tsohon shugaban kasar ya karfafa masa guiwa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kogi.

A wata takardar taya murna da Gwamnan ya aikawa Obasanjo, wanda kakakin Gwamnan Onogwu Mohammed ya fitar ya bayyana tsoron shugaban kasar a matsayin mai kishin kasa da son cigaban yankin Afrika

- Advertisement -

Sanarwar ta kara da cewa Obasanjo mutum ne mai cike da basira da dogon tunani wanda ya goge wajen lamurran da suka shafi sha’anin mulki  da tsaro da jagoranci nagari

Yahaya Bello ya yi addu’ar Allah ya raya Obasanjo ya albarkaci rayuwarsa domin cigaba da anfanar da jama’a

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: