YAJIN AIKIN ASUU: Mafita Ga Daliban Najeriya

Ra’ayin: Aliyu Samba

Ina kira ga dalibai na jami’a da suyi kwasa kwasai ta yanar Gizo (Online Courses) dan samun cigaban karatun su. Har degree da Masters da PhD zaku iya yi, dan a yanzu ina da certificate na kwas yafi 10 duka online. Kuma da kudi kadan zaka yi karatun ka, ka fahimta, ka kuma samu takardar sheda wacca duk duniya zaka nuna ta.

Wani lokaci akwai wanda ya ga CV na sai ya kirani yace ai bai sanni a UK ba, Kuma yaga nayi wasu kwasa kwasai a Metropolitan School Of Management Studies dake UK, sai na dauko masa kwafi na shedar kammalawa yayi ta mamaki, sai da na ce masa ta yanar gizo nayi, sai yake cewa lallai wato akwai damammaki a hannun mu, mu muke watsar wa.

Kuma haka ne, akwai manajoji na waya da zaka sauke daga Play Store kayi rejista kuma ka yi karatu a dukkan mataki da kake so, saidai munfi shagala da kallon kwallo, hirarraki, nishadi, musu, cece kuce, tada zaune tsaye da kuma yada hotuna a soshal Midiya maimakon mu amfani kanmu da wannan dama da takanolagi ya kawo.

- Advertisement -

Ina shawartar ku da kuyi amfani da wannan dama, masu degree, Masters da Post graduate courses, har ma da masu PhD suyi amfani da wannna dama, ba sai mun takura kanmu da shiga damuwa ba saboda yajin aikin ASUU. Zaka iya karatu har a Harvard University kana nan Kano a gidan ka. Kwanan nan nayi course dasu, a yanzu ma akwai tayin PhD daga UK, Kawai rejistar zanyi da an fara mu shiga. Kada mu bari damar nan ta wuce mu.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: