Za Mu Bada Tukuici Don Kama Yan Bindiga- Gwamnatin Neja

Za Mu Bada Tukuici Don Kama Yan Bindiga- Gwamnatin Neja

Gwamnatin jihar Neja ta ce ta ware kaso mai tsoka ga duk wanda ya taimaka mata da muhimman bayanai da zai sa ta kai ga sanin inda ƴan bindiga ke buya ko waɗanda suke taimaka musu.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Tsaron Cikin Gida Emmanuel Umar ne ya sanar da hakan.

Wannan na zuwa ne ƴan awanni da gwamnatin ta fitar da sanarwar nasarori da ta samu na hallaka sama da ƴan ta’adda 200 a jihar a ƴan kwanaki uku da suka gabata a wani aiyyukan haɗin gwiwa na jami’an tsaro.

- Advertisement -

Ya ce, “mun san yanzu ƴan ta’addan nan sun buya cikin al’umma a daidai lokacin da jami’an tsaron mu ke ci gaba da yi musu luguden wuta a faɗin jihar nan. Muna sanar wa Jama’a cewa duk wanda ya sanar da mu bayanai da za su sa mu kai ga kama ɗan bindiga ko mu samu bayanai na waɗanda suke taimaka musu (Informants) ko waɗanda suke adana musu makamai, gwamnati ta yi alƙawarin bada kyakyawan tukuici ga duk wanda ya sanar da ita”.

Kwamiahinan ya sake tabbatar mana da cewa ko da yamman nan jami’an tsaro sun sake yin nasarar hallaka aƙalla ƴan ta’adda 100 a ci gaba da yi musu luguden wuta a faɗin jihar.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: