2023: Milyan 100 ne kudin fom din takarar shugaban Ƙasa a jam’iyyar APC
-Kudin fom din takarar shugaban kasa milyan N100m
-Gwamna milyan N50m
-Sanata milyan N20m
- Advertisement -
-Majalisar dokoki miliyan N10m
-Majalisar jiha Milyan N2m
Uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta sanar da sanya farashin Naira miliyan 100 a matsayin kudin fom din tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar a zaben 2023
APC ta yanke hukuncin ne a yayin babban taron shuwagabannin jam’iyyar da ya gudana yau Laraba a Abuja,
Muryoyi ta ruwaito APC ta tsaida Naira Miliyan 50 kudin fom din neman Gwamna sai Naira Miliyan 20 na sanata sai Naira Miliyan 10 kudin fom din Dan Majalisa sannan Naira miliyan 2 kudin fom din Majalisar dokoki ta jiha.