Ba zan bari wani ya lalata Najeriya ba -inji Shugaba Buhari 

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ranar Talata a Abuja ya bukaci Ƴan-Nijeriya da su ƙaurace wa bada hadin kai wa wakilan dake janyo taka doka da oda a Ƙasar nan, ya bada tabbacin babu wani mutum ko kungiya da za’a zuba ido a barta ta Hargitsa Najeriya.

“Muna da Ƙasa mai kyau, muna da arziki, kuma muna da tarin Al’umma, to amma bansan mai yasa butane ke bari ayi amfani dasu gurin neman Hargitsa Kasar su ba,” Shugaban ya fadi hakane a yayin Liyafar buda baki da Gwamnoni, Ministoci da Shugabannin Hukumomin Gwamnati.

Shugaba Buhari, wanda yayi Godiya wa Gwamnoni da Ministoci gameda amsa gayyatar buda bakin Azumin watan Ramadan, ya bayyana Ƙwarin gwiwar cewa Kasar Zatayi nasara duk da ƙalubale tsaron da ake ciki.

- Advertisement -

Gameda Babban zabe dake tafe, Shugaban ya kara Jaddada cewa kasan cewar sa, wanda ya amfanu da gamsassen zabe mai cike da Adalci, ta hanyar yin amfani da fasahar zamani da samar da katin zabe na Dindindin, ba abu ne da zai sake yiwuwa, ga wani ya wawushe kuru’un Miliyoyin Mutane a Ƙasar nan ba.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya yabawa Shugaba Buhari kan yadda ya Ƙudura tserar da samar da mafita a wani lokaci mai Muhimmanci cikin tarihin Najeriya.

“Mun dace da Shugaban da baya Shagaltuwa kan ƙalubale na yanzu yanzu, ya kan tsaya ya ci gaba da zage damtse Gurin sabunta Kasar mu, saboda da haka muma Gwamnoni da Ministoci da Shugabannin Hukumomin Gwamnati haka muke sadaukar da kan mu Gurin gina Ƙyakƙyawar Ƙasar Najeriya.

Ya nuna cewa Wannan Karo Watan Ramadan Mai Girma yazo a dai dai lokacin da aka kammala lokacin mai Muhimmanci ga Kiristochi, Gwamnan jihar Ekiti yace, lokaci dake da Daraja Gurin sabunta alfanu war, Sadaukarwa, bada Sadaka, Yafiya, da samun sauki ga ɗaiɗaikun Mutane dama kuma Ƙasa.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: