DA DUMI-DUMI: An ga wata Ramadan a Saudiyya gobe Asabar Azumi
Daga Muryoyi
Hukumar kasar Saudiyya ta bayyana cewa an ga jinjirin watan Ramadan a kasar Saudiyya a wajaje da dama.
A saboda haka gobe Asabar 2 ga watan Afrelu 2022 ya kama daidai da 1 ga watan Ramadan 1443 A.H
- Advertisement -
Sai dai a Najeriya ana dakon mai alfarma Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar ganin wata ko akasin haka a Najeriyar ganin cewa sai anjima za a duba watan a kasar ta Najeriya