Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Jam'iyyar APC Kaduna za tayi tankade da rairayen yan takaran...

DA DUMI-DUMI: Jam’iyyar APC Kaduna za tayi tankade da rairayen yan takaran Gwamna

Jam’iyyar APC Kaduna za tayi tankade da rairayen yan takaran Gwamna

Daga Muryoyi

A yayin da zaben fitar da Gwani na jam’iyyar APC ke kara karatowa an fitar da rahotannin cewa APC Kaduna ta kafa Kwamiti akan masu neman takaran kujeran Gwamnan a jahar a karkashin inuwar jam’iyar APC.

Bayanai sun ce cikin ayyukan da Kwamitin zai yi sun hada da maida hankali akan mahimman abubuwa kamar haka:

- Advertisement -

1. Jin ra’ayoyin jama’ar jahar Kaduna akan kowane dan takaran kujeran Gwamnan Jahar a APC.

2. Shirya mahawara tsakanin yan takarkarun wato debate.

3. Gudunmuwan da kowane Dan takara yakawo wa jahar Kaduna karfin yafara neman takaran.

4. Duba dabi’un kowane dan takara, Wanda zai iya zamowa abin koyi ga jama’ar jahar Kaduna masu kyau.

5. Yanayin ma’amula da zaman takewan kowane dan takara tsakanin shi da al’umma jahar Kaduna.

6. Kwarewa da gogewa akan iya tafiyar da aikin gwamnati, duba da cewa jahar Kaduna itace cibiyar Arewacin Nigerian ne.

Wadannan sune kadan daga cikin ayyukan da kwamitin zai yi…

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: