Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Sanata Dan Sadau yace sun kori Sheikh Nuru Khalid daga...

DA DUMI-DUMI: Sanata Dan Sadau yace sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin Masallacin Apo gaba daya

DA DUMI-DUMI: Sanata Dan Sadau yace sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin Masallacin Apo gaba daya tunda bai yi nadama ba

A yayin da ake rade-radin cewa an mayar da Digital Imam mukaminsa na limanci a masallacin Apo, kwatsam sai gashi Sanata Sa’idu Muhammad Dan Sadau shugaban kwamitin Masallacin na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin ne gaba ɗaya.

Sanata Dan Sadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.

A wata wasiƙa da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sanata Dan Sadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce an ɗauki matakin korarsa ne gaba ɗaya saboda ƙin yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ɗin.

- Advertisement -

Wasiƙar ta ce: “Aaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi’ar mutum.

“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka faɗa.

“Shugabanci na buƙatar sauke haƙƙi ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun ɓata wa ƴan ƙasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na ɗaukar matakin da ya dace saboda al’umma.

“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara huɗubar ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: