DA DUMI-DUMI: Yahaya Bello yasa an bindige gungun masu garkuwa da suka addabi jihar Kogi

Yahaya Bello yasa an bindige gungun masu garkuwa da suka addabi jihar Kogi

Daga Muryoyi

Jami’an tsaro da yan banga sun kai hari mabuyar masu garkuwa da mutane inda suka kashe akalla 2 daga cikinsu kana suka raunata wasu a karamar hukumar Ofu dake jihar Kogi.

Muryoyi ta ruwaito tun da farko yan bindigar sun addabi kauyakan garin wanda hakan tasa yan banga tare da hadin guiwa da Jami’an tsaro sukayi wani binciken sirri tare da gano sansanin mayakan.

- Advertisement -

Bayan gano mabuyar yan bindigar ne a Ochadamu sai yan banga suka kai masu farmaki da tsakiyar daren ranar Laraba suka halaka biyu sannan aka kama wasu 3 kuma suka tsere da raunuka.

Muryoyi ta ruwaito an shafe fiye da awa guda ana fafatawa da masu garkuwa kafin akarshe aka cimma nasarar kama wasu da kashe wasu.

Tuni dai Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ya jinjinawa gamayyar Jami’an tsaro da yan bangar bisa wannan namijin kokari.

A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Onogwu Muhammed ya fitar yau Laraba yace Gwamnan ya horesu da su kara zage damtse suyi aiki tare domin ganin ba a sake samun bullar wani ayyukan ta’addanci a ko ina a fadin jihar ba

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: