DA DUMI-DUMI: Yan Bindiga sun kai hari gidan Rediyo ana tsaka da gabatar da shirye-shirye
DA DUMI-DUMI: Yan Bindiga sun kai hari gidan Rediyo ana tsaka da gabatar da shirye-shirye
Daga Muryoyi
Yan bindiga sun kai hari a gidan Rediyon Fresh FM dake Ibadan ana tsaka da watsa shirye-shiryen safe.
Muryoyi ta tattara rahoton cewa yan bindigar sun kutsa gidan Rediyon ne da sanyin safiyar yau Lahadi kuma sukayi awon gaba da muhimman kayyakin aiki.
- Advertisement -
Kodayake dai babu rahoton jikkata kowa ko kashe kowa amma dai sun tarkata kayyaki masu muhimmanci da ba a kayyade adadinsu ba.