Ganduje ba kyau!

Ganduje ba kyau!

Wato maganar gaskiya Moddibo Ganduje ya shammaci ‘yan takara. A cikin weekend ya basu awa is ishirin da hudu su aje aiki? Gaskiya wannan dibar kafa da yawa take, bai bari sun kai Monday ba, balle su dan gama ‘yan cuku cukunsu a office, su dan rurrufe abinda zasu iya rufewa, kawai ya buga musu kararrawar tashi 😅

Akwai kyakkyawan zaton cewar dukkan mutanan da Gwamna ya umarta su aje aiki in suna son yin takara, a cikinsu babu dan takararsa na Gwamna. Na tabbata idan da yana da dan takara a cikin wadan da suka sauka, da ba zai masa wannan shammatar ba, a kalla a barshi ya sauka a nitse.

‘Yan takara duk sun saki jiki cewar an ki karbar resignation din Jan zakara, dan haka suma zasu Mike kafa, su cigaba da wadaka suna warisa a cikin lalitar Gwamnati, ashe ashe basu san cewar Moddibo idonsa biyu akansu ba, kar yake kallon kowa.

- Advertisement -

Koma dai meye Moddibo yace tsiyar Nasara sai zashi gida. Kun san ai da Nasara ya tashi, yana da ma’aikata da yawa, masu dafa abinci da direbobi da masu shara da masu ban ruwan fulawa da masu gadi da sikiuriti da sauran barori. Da lokacin tafiyar Nasara ya kusa, ma’aikatansa sukai ta murna zai koma garinsu.

Kan kace kwabo ma’aikatan Nasara sun shiga yin watanda da kayan gidan Nasara. Wani yace ai idan Nasara ya tafi shi zai dau kujeru, wani yace kufunan shayi, wani yace talabijin da radio, wani kuma yace ai mota kaza zai dauka, haka dai sukai ta rabo tsakanin su, har lokacin tafiyar nasara yayi.

Ma’aikata basu sani ba, ashe Nasara ya sayar da komai na gidansa. Ranar da zai tafi baki suka cika gidansa, can sai Nasara ya leko yace ina wanda ya sayi kujeru, ace gani nan, sai yace zo ka dauka, haka nan, ina wanda ya sayi mota, Shima yace gani, haka nan, Nasarar ya sayar da komai na gidan, sai ya zama daga shi sai jakarsa ta tafiya. Nan dai Nasara ya bar ma’aikatansa da sallallami. Ashe basu san tsiyar Nasara sai zashi gida ba. Dan haka, a kiyayi tsiyar Moddibo Nasara.

Yasir Ramadan Gwale
18-04-2022

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: