Gwamnati ta gaza: Hadiza Bala ta koka game da matsalar tsaro a Najeriya

Daga Muryoyi

Tsohuwar shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa Hadiza Bala Usman ta caccaki Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan gazawa wajen tsare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya

Muryoyi ta ruwaito a wani sako da Hadiza ta fitar ta shafinta na Facebook ta yi kira ga Gwamnatin ta kara daura damara wajen yin abunda ya dace kan tabarbarewar tsaro

A cewar ta “Yau shekara 8 kenan da aka yi garkuwa da yan mata Chibok 276 a makarantarsu, har yau ragowar 109 na cen a hannun masu garkuwa.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito a sakon na Hadiza ta cigaba da cewa ‘Ana sace mutane da dama maza da mata manya da kanana a garuruwa, kauyaku an tare hanyoyi an yi garkuwa da matafiya….

Dole ne a tashi tsaye a kawo karshen wannan rashin tsaro dake ta kara yaduwa… ba zai yiwu mu cigaba da rayuwa a haka ba…

A kubutar da yanuwanmu da aka sace a kawo mana ingantaccen tsaro a kasarmu, shine kukan mu kuma shine abunda muke nema…

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: