Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuGwamnatin jihar Kogi ta hana cin naman shanu a fadin jihar

Gwamnatin jihar Kogi ta hana cin naman shanu a fadin jihar

Gwamnatin Kogi ta binne shanun da su ka ci guba, inda ta hana cin naman shanu tsawon mako ɗaya

 

A jiya Juma’a ne Gwamnatin Jihar Kogi ta bada umarnin binne sauran sassan jikin shanun nan da a ka gano sun mutu sakamakon cin wani abu da a ke zargin guba ne a garin Lokoja.

 

Gwamnatin ta kuma umarci al’ummar garin Lokoja ɗin da su kaurace wa xin naman saniya har tsawon mako ɗaya domin guje wa cin naman shanun da a ka ce tuni ya na ta zagaya wa akasuwa.

 

“Gwamnati na ƙoƙarin binne shanu da yawa da abin ya shafa amma ba dukkan su ba,” in ji wani jami’in gwamnati.

 

- Advertisement -

Da ya ke magana a kan lamarin, Kwamandan Hukumar Tsaro mai Kare Fararen Hula, NSCDC, Suleman Marafa ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAHCON a Lokoja cewa tuni a ka kai samfurin naman dakin gwaje-gwaje.

 

Ya ce “dakarun kula da gonaki da haɗin gwiwa da sashen kula da shanu da lafiyar dabbobin na Ma’aikatar Noma ta jihar da kuma sashen tsafta na Ma’aikatar Muhalli sun yi gwaji s kan sassan jikin shanun.

 

“Gwajin ya tabbatar da cewa shanun sun ci guba ne kuma ɗan adam ba zai  iya cin naman ba.

 

“Hakazalika Gwamnatin Kogi ta na mai shawartar al’umma, musamman na Lokoja da su dakata da cin naman shanu na a ƙalla tsawon mako ɗaya,” in ji shi.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: