Idan da kunya, akuyoyin kan titi da bazasu ce uffan akan Malama Zainab Ja’afar Mahmud ba

Idan da kunya, akuyoyin kan titi da bazasu ce uffan akan Malama Zainab Ja’afar Mahmud ba.

Wato wasu yan matan Facebook da muke kauda kai daga tsiyar da suke tabkawa na bayyana tsiraici, anan Facebook sun dauka sunci gari, wai har zasu iya magana akan kamila, yar kamili, matar kamili, wacce ta rungumi aikin fassara littafin Allah Alkur’ani mai girma.

Sai ga wata can almajirar akuya a wajen tsiraici, sai tazo tana bude bakinta mai wari tanayiwa malama Zainab habaici,, da cewa, “ai muryar ta ma tsiraici ne oh wallahi nayi mamaki ace almajiran akuyoyi a wajen wayewa, tazo tana suka.

Dayake hassada ya cika mata zuciyarta ga wata mace acan masallaci, tana aikin Allah, yayinda ita kuma tana can gantali, daga ofishin oga wane sai dakin wane.

- Advertisement -

Bai kamata a bawa wadannan Almajiran akuyoyi amsa a addinan ce ba, abi salonsu a durfasu har su gane asalin shayi ruwa ne.

Abun mamaki ita mai sukar fa, babu irin shiga ayi gogayya da maza da gyalle a yafe a kafadu da batayi ba, anyi gantalin gwagwarmayar siyasa babu wani hazo da ba’a keta dasu ba, yanzu idan ita bata zama abun zargi ba, ai malama zainab ko kusa bazata zama ba.

Abun mamaki wani sa’in sai in tambayi kaina wai matan nan da suke yawon gantali ayi hoto da wannan ayi da wancan, koma aje gun Mai hoto ayi, kuma azo social media a yada, kirji a waje wuya a waje, fuska an danno hoda ko dadin gani babu, azo a saka wasu kattin banza suzo suna kuka kamar karnuka wow, wow, basu da iyaye ne da zasu iya ce musu kulll ne? Kodai sunfi karfin iyayen ne? Kodai suma iyayen hakane,, na jeka nayika?

Daga Muhammad Ismail Ali.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: