Idan kana neman ‘yayan da Iyayensu suka haifa suka kasa kula dasu, to ka taho masana’antar fim –inji Sarkin Waka

Idan kana neman ‘yayan da Iyayensu suka haifa suka kasa kula dasu, to ka taho masana’antar fim –inji Sarkin Waka

Daga Muryoyi

Sarkin Waka Naziru Ahmad ya sake jefa wata maganar wacce ake kallo tamkar martani ne yayi wa wasu daga cikin jaruman masana’antar fim da a kwanan nan suka taso maganar almajiranci a gaba.

Anji yadda wasu daga cikin matan fim ke sukar batun Almajiranci, to sai dai Naziru a wani sako da ya fitar yace “Ba Almajirai ne ‘yayan da Iyayensu suka haifa suka kasa kula dasu ba. Idan kana neman ‘yayan da Iyayensu suka haifa suka kuma kasa kula dasu, to ka taho masana’antar fim!

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito mawakin ya cigaba da cewa “Wannan shine gaskiya malanmai Ko tayi dadi ko kar tayi dadi. Kowa ya dauko sharrinsa sai kan almajirai da iyayensu??

To mu munsan abunda kuke kira da almajirci duk da ba sunansa kenanba musan niyyar da ke sa iyaye su kai yayansu mun kuma ga amfaninsa, wato kunfiso a bar yara a daji babu manufa aiyita basu bindigu suna kashe mune wannan shine burinku??
wannan shine kawai. Ayi hakuri damu!

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: