Mun sauke Sheikh Nuru daga limanci ne saboda tsoma baki da yake yi a harkokin siyasa –inji Shugaban Kwamitin Masallacin APO
Shugaban kwamatin masallacin Apo Quarters dake Unguwar Apo a Abuja, tsohon Sanata daga Jihar Zamfara, Sanata Dansadau ya ce:
“Dalilin da yasa suka sauke, Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallaci, shi ne tsoma bakinsa da yake yi a cikin harkokin siyasa, yin hakan kuma ba aikin sa bane,”
Sanata Dansadau ya kara da cewa “sun sha fada masa abun da suke so ya dinga fada a huduba amma ya ki kiyaye wa”
- Advertisement -
‘Yan Najeriya dai na Allah-wadai da korar Sheikh Nuru Khalid daga limanci kan sukar Buhari