Ranar Jana’izar Jam’iyyar APC zata kasance…

Ranar Jana’izar Jam’iyyar APC zata kasance…

Daga M Inuwa MH

Lokacin da aka gabatar da zaben fidda gwani na jam’iyar APC a Jihar Lagos a 2015 bayan samun Nasara da Shugaba Buhari yayi akan Sanata Rabi’u Musa kwankwaso da Atiku Abubakar da Sam Nda Isaiah, jiga-jigan jam’iyar sun zauna suka yanke shawara da cewa Bola Ahmad Tinubu ya kawo mataimakin Shugaban kasa daga Bangaren sa, nan take Bola Tinubu yace aikuwa babu wanda zai kawo daya wuce ya kawo kansa da kansa ma’ana shine mataimakin Buhari yana fa’din haka sai Sanata Abubakar bukola Saraki ya mike Yace mu ba za muyi Muslims-muslims ba a wannan jam’iyar tamu ta APC daman can ana sukarmu da cewa APC jam’iyar musilmai ce Ina ga yanzu Kuma ace Shugaban kasa da mataimakin sa duk musilmai ne? Nan dai aka goyi bayan Saraki aka ha’du aka danne Bola Tinubu aka Kuma matsa masa ya kawo sunan mataimakin Shugaban kasa shine ya kawo sunan farfesa Yemi Osinbanjo.

A halin yanzu shugaba Buhari bashi tare da Bola Tinubu shi kansa Bola Ahmad Tinubu tuni yasan da Hakan Kasancewar sa dan takara mafi karfi yana da tsari PLAN kala-kala daga A.B C har zuwa Z duk Bola Tinubu nada wannan Plan, tsarin sa na farko shine dogaro da Buhari da yarjejeniyar su da jam’iyarsa APC a lagos na Cewa za’a bashi takara a zaben 2023 Kai tsaye bayan Buhari ya gama Mulki haka yasa ya goyi bayan Buhari 2015 da Kuma 2019 ba tare da wani shakku ba a halin yanzu jam’iyar APC da Shugaba Buhari sunyi watsi da alkawarin da suka ga Bola Ahmad Tinubu Hakan yasa ya Kai tsaye ya tafi Tsari na Gaba wato wato PLAN B.

- Advertisement -

A tsarin PlAN B Bola Tinubu zai yi anfani da karfin ku’di tare da karfin jiga-jigan masu rike da Gwamnatin wanda shi ya kafa domin irin wannan lokaci na neman samun tikitin takara na jam’iyar ta APC wanda yanzu Haka yana kan anfani da wannan tsari na PLAN B wanda Kuma babu alamun zai yi tasiri.

Idan Bola Tinubu ya samu nasarar zama Shugaban kasar Nageriya tabbas zai toni Asirin Shugaba Buhari watakila ma ya turashi zuwa gidan yari domin shima Tinubu irin Zuciyar Buhari ne dashi yana da son Kai bashi da yafiya Kuma yanzu Yana kallon Buhari amatsayin maciyin amanarsa shima Buharin ya fuskanci haka wannan dalilin yasa Buhari ba zai aminta da Bola Tinubu ya samu tikitin tsaya takarar ba.

Wasu Gwamnoni sun zuga Osinbanjo ya fito takara domin cimma wani buri nasu kafin zaben fidda gwani dukda cewa Osinbanjo Yana matukar tsoron tsohon Mai gidan nasa amma dai yayi karfin hali ya fito Bisa dogaro da karfin Gwiwar da ake bashi.

Binciken Sirri na Cewa Shugaba buhari da jam’iyar APC sun zabi Rotimi Ameachi amatsayin wanda zaiyi wa jam’iyar takara a zaben 2023.

Wasu Gwamnoni tare da ire iren su gwamna Yahaya bello na kogi tuni sunyi watsi da kudrin na jam’iyar APC da Kuma Shugaba Buhari Kuma suna cigaba da yakar wannan kudri ta Karkashin kasa.

Har’ila yau wasu gwamnoni tare da sanatocin jam’iyar APC dake kudu maso yamma da kudu maso gabas sun ha’du sun ha’da Kai sun ware suna cewa dole ne shugaban kasa ya fito daga yankin su.

Bayan zaben fidda gwani na jam’iyar APC a cikin wa’yan nan bangarori na jam’iyar da ko wanne ke da karfin gaske babu wani bangare da zai goyi bayan wani bangare domin kawai jam’iyar tayi nasara a Babban zaben 2023 mai zuwa har ‘ila yau alamu sun nuna cewa ko wanne bangare zai Iya fita daga jam’iyar Kai tsaye bayan zaben na fidda gwani wa’yanda Kuma suka rage za’a Yaki jam’iyar tare dasu suna cikin jam’iyar ba tare da sun fice ba ma’ana zasuyi Anty-Party domin ganin APC ta Fadi zaben na 2023.

Shiyasa muke hasashen cewa Ranar zaben fidda gwani zata kasance Kuma ranar JANA’IZAR jam’iyar ta APC.

Ku zuba Ido lokaci na zuwa shine alkalinmu daku Daga M Inuwa MH…

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: