Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuShugaban kasar Ukraine ya roki ya gana da Shugabannin Afrika don su...

Shugaban kasar Ukraine ya roki ya gana da Shugabannin Afrika don su taimakawa kasarsa a yaki Rasha

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bukaci taimakon kungiyar Tarayyar Afirka, domin mara masa baya kan mamayar da Rasha ta yi kasarsa, inda ya bukaci yi wa kungiyar jawabi.

Mr Zelensky ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa ya kira shugaban Senegal Macky Sall a ranar Litinin, kuma a tattaunawarsu sun tabo batun matsayar Afirka a sanarwar da ta fitar a watan Fabrairu tare da bukatar Rasha ta dakatar da bude wuta tare da hawa teburin sulhu.
A tattaunawar ta wayar tarho, Mr Zalensky ya shaida wa Macky Sall yadda Ukraine ke fadi-tashi da kokarin kare kasar daga hare-haren Rasha.

Tarayyar Afirka dai ta nuna rashin jin dadi da amincewa matakin da Rasha ta dauka a Ukraine.

Kuma Senegal na daga cikin kasashe 17 na Afirka da suka rattaba hannu a Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar Rasha ta kawo karshen yakin sojin da take yi a kasar.

- Advertisement -

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: