TO FA: An hako gawar Basarake Alaafin of Oyo bayan musulmi sun gama yi masa jana’iza

Daga Muryoyi

Rahotanni daga jihar Oyo na bayyana cewa an hako gawar margayi Alaafin of Oyo Oba Lamidi Adeyemi jim kadan bayan kammala yi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito masu bin gargajiya wato yan addinin gargajiya na Sango ne suka hako shi domin yi masa tasu jana’izar kamar yadda al’adar kasar Yarabawa ta tanadar

A yau Asabar ne dai babban Limamin jihar Oyo, Mas’ud Adebayo, da wasu jiga-jigai a jihar da sauran dandazon Musulmi sukayi wa margayin sallah sannan aka bizne shi.

- Advertisement -

Sai dai daga bisani yan kabilar Sango sun hako gawar daga inda aka bizne shi a Ode Aro wani sashi na makabartar sannan suka tafi da gawar zuwa wani waje na daban suna yi masa tasu jana’izar.

Muryoyi ta ruwaito nan da nan suka kori yan jarida da sauran masu zaman makoki daga ganin yadda zasu gudanar da jana’izar.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: