Wanda duk kake ganin azzalumi ne, ka nemi katin zabe ka kore shi a 2023 wanda duk kake ganin mai gaskiya ne ka nemi katin zabe ka shigo dashi a 2023 –inji Sheikh Maqari
Daga Muryoyi
Babban Limamin Masallacin Abuja Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari ya yi kira ga al’ummar Najeriya musamman musulmi suyi karatun ta natsu a 2023 wajen fitowa kwansu da kwarkwatansu suyi zabe
Muryoyi ta ruwaito Sheikh Ibrahim yayi wannan kiran ne a lokacinda yake sharhi kan hudubar da Babban Limamin Masallacin Apo Quarters yayi a kwanakin baya, Sheikh Nuru Khalid na cewa talakawa kada su fita zabe muddin yan siyasa suka kasa hana salwantar da jinanensu da dukiyoyinsu.
- Advertisement -
Sai dai Shehin Malamin ya ce ya kamata mu natsu muyi tunani akan cewa ko anyi zabe ko ba ayi ba a ranar 29 ga watan Mayu dole ne a rantsar da wani a matsayin shugaban kasa da Gwamna da sauran kujeru.
Ya ce yasan Sheikh Nuru ba da son zuciya yayi wancen kiran ba to amma kiran ya taimaka wa masu son yin magudi ko dauri dora wa talkawa gurbatattun shuwagabanni wadanda zasu cigaba da gasa masu aya a hannu. Ta hanyar mallakar katin zabe da fitowa mu jefa kuri’a ce kadai zamu kawo sauyin da muke so.
“Don haka don Allah muyi hakuri wanda duk kake ganin azzalumi ne, ka nemi katin zabe ka kore shi a 2023 wanda duk kake ganin mai gaskiya ne ka nemi katin zabe ka shigo dashi a 2023” –inji Sheikh Praf. Ibrahim Maqari