Wani babban mutum a Kano yaki karban kayan lefen diyarsa yace a rage kayan ko a fasa auren

Wani Babban mutum a jihar Kano aka kawowa ‘yarsa lefe akwati goma sha biyu banda kits, aka Kira shi ya gani, yace wallahi bazai karba ba, sai an mayar

Aka kada aka raya yace sai an mayarda kayan.

Ko kun San dalilinsa :- cewa yayi

1) Yata ba sayarda ita Zan yi ba. So nake tayi aure a matsayin ibada ba holewa ba.

- Advertisement -

2) Kuma yata tana da kanne yammata, shike nan sauran kannenta sai su sa rai suma sai an kawo musu akwati goma sha biyu ko sama da haka, kuma idan Allah bai horewa mijin ba, su raina shi. Suga ya gaza.

3) Suturar da ya zuba acikin lefen masu tsadar gaske, duk iyayensa da suka kawo lefen babu wacce tasa mai tsadar su, me yasa ya kasa siyawa iyayensa su sa kafin ya siyawa yata, idan mai arziki ne shi ba makaryaci ba.

4) Da ace rabin kudin kayan lefen, abinci ya siya, Shekara nawa zasu yi suna cin abincin shi da Matarsa kafin ya kare.

5) Yanzu da yai wannan lefen ya nunawa yata shi Mai arziki ne, idan zama yai zama tsakaninsu har ta gane abinda take zato ba haka bane, yana ganin zai yi mutunci a idonta.

6) Shike nan yana so yata ta ringa alfahari acikin kawaye cewa babu wacce aka yiwa lefe kamar nata, Wanda hakan zai jawo mata kiyayya da hassada a tsakanin kawayenta, kuma shi kansa alfaharin haramun ne.

7) Yana daga cikin aladar da ta haddasa zinace zinace a kasar Hausa, domin samari basu da wadatar hada kayan lefe. Gara su kebe da yan matan nasu yafi sauki.

Na fada kuma babu canji ko dai a rage lefe ko kuma a dakatar da maganar aure har sai lokacin da shi da iyayensa suka fahimci abinda nake nufi.

Idan an rage lefen anyi biki ta tare, idan yana so ya siyo mata kantin kwari ta ajiye a dakinta babu ruwa na, matarsa ce.

Daga TJ Zarewa

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: