YANZU-YANZU: Sarkin Musulmi ya sanar a hukumance cewa ba aga watan Shawwal a Najeriya ba….
Assalaamu alaikum,
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ayyana ranar Litinin 2 ga watan Mayu 2022 a matsayin ranar Sallah sakamakon ba aga watan Shawwal a yau Asabar ba a duka fadin Najeriya
Muryoyi ta ruwaito babu wani rahoton ganin wata sahihi daga Masarautu ko kwamitin ganin wata saboda haka gobe za a tashi da azumin, wato za a cika azumin 30.
- Advertisement -
Ranar Litinin zai zama 1 ga watan Shawwal shine ranar karamar Sallah