DA DUMI-DUMI: Hukumar NDLEA ta kama Ameachi da hodar Iblis a filin jirgin samanPort Harcourt

Hukumar NDLEA ta kama Ameachi da hodar Iblis a filin jirgin saman Port Harcourt

Daga Muryoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta kama Okechukwu Francis Amaechi, bisa zargin shigo da hodar iblis a filin jiragen sama na Port Harcourt.

NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Lahadi cewa Okechukwu tsohon mai laifi ne wanda ya gama zaman gidan yari a kasar Brazil an sako shi kenan a watan Maris din shekarar 2022 da muke ciki bayan ya kammala wa’adin sa na zama a gidan yarin Brazil.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito an kama Okechukwu da koken wato hodar Iblis da nauyinta ya kai 4.56kg ya boye a tayar mota ya shigo da ita daga Brazil.

Hukumar ta kuma ce ta kama kwayar Tramadol 37,876 da kwalaben kodin 10,884 da taba wiwi kilo 825.016 a jihohin Zamfara da Kogi da River da Kaduna da kuma Kano

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: