Al-Mustpah ya lashe zaben fidda Gwani …shine yayi alkwari zai koma Sambisa da zama idan yaci zabe

Al-Mustpah ya lashe zaben fidda Gwani …shine wanda yayi alkwari zai koma Sambisa da zama idan yaci zabe

Daga Muryoyi

Tsohon dogarin Sani Abacha Manjo Hamza Al Mustapha, ya lashe zaben fidda Gwani na shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance wato AA

Al-Mustapha yasha alwashin zai koma Dajin Sambisa da zama middin aka zabe shi shugaban kasa domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya. Sannan ya ce cikin kankanin lokaci zai yi amfani da kwarewarsa wajen kawar da duka wasu ayyukan yan bindiga a fadin Najeriya.

- Advertisement -

Muryoyi tq ruwaito Al-Mustapha ya samu kuri’u 506 a yayinda abokin karawarsa Chief Samson Abiodun Odupitan, ya samu kuri’u 216 a zaben da jam’iyyar tayi a yau Alhamis a Abuja.

Yan takara Hudu ne suka fafata a gasar sai dai kafin soma zaben sai yan takara Biyu, Tunde Kelani da Chief Osakwe Johnson suka janye wa Al-Mustapha

Deligate 854 ne aka tamtance su kada zabe a zaben fidda Gwanin.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: