Thursday, March 23, 2023
HomeBatutuwaAdabiAn kama kunshin makamai da aka shirya kai hari a Kano da...

An kama kunshin makamai da aka shirya kai hari a Kano da ka iya zama mafi muni a Najeriya – inji hafsan tsaro

An kama kunshin makamai da aka shirya kai hari a Kano da ka iya zama mafi muni a Najeriya – inji hafsan tsaro

 

Daga Muryoyi

 

Shugaban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya fallasa cewa Jami’an tsaron Najeriya a makon da ya gabata sun daƙile wani yunƙurin kai hari a Jihar Kano, “wanda ka iya zama mafi muni” a ƙasar,

 

A wata tattaunawa da yayi da Chennels TV domin ranar Dimokuradiyya a yau Lahadi Janar Irabor ya ce an daƙile harin ne a Kano a cikin makon da yan bindiga suka kai wani hari kan wata cocin Katolika a garin Owo na Jihar Ondo, wanda suka kashe mutum fiye da 40.

 

- Advertisement -

Shugaban hafsan sojin ya kuma ce sun samu nasarar daƙile harin ne da ka iya zama mafi muni a Najeriya saboda bayanan sirri da suka samu kuma suka gaggauta daukar mataki akai.

 

Irabor ya ce “A lokacin mun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su. Mun ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasa, har da Abuja.”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: