Anyiwa Saurayi da Budurwa bulala a bainar jama’a bayan kama bidiyonsu suna zina
Wani saurayi da budurwa a kasar Ghana sun sha bulala a hannun matasa a bainar jama’a bayan da bidiyonsu ya bayyana akan yanar gizo suna lalata.
Hakan ya jawo cece-kuce daga bangarori daban daban kowa na bayyana ra’ayinsa, wasu na ganin hakan bai dace ba wasu kuma na ganin hakan ya dace domin zama izina ga yan baya ko kuma masu son su kwaikwayi wannan mummunar dabi’a.
A bidiyon dai an ga yadda matasan suka daure Saurayi da budurwar a jikin wani karfe a kofar fadar Sarki a Ghana, aka samu wasu katti suka dauki bulala suka rika zane su a bainar jama’a suna kirgawa.
- Advertisement -