Azabar Allah na jiran waɗanda suka kai hari suka kashe mutane a cocin Ondo –inji Buhari
Daga Muryoyi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwa da bakin ciki game da kisan gillar da akayiwa wasu masu ibada a coci da sanyin safiyar yau inda yan bindiga suka afka masu suka kashe mutane da dama suka jikkata wasu sannan sukayi awon gaba da wasu da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Muryoyi ta ruwaito Shugaba Buhari na cewa baƙin ciki na har abada yana jiran waɗanda suka kai wannan hari duniya da lahira, kuma zasu gamu da azabar Allah tana jiransu a lahira.
- Advertisement -
Shugaban kasar ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar Ondo da yan’uwa da abokan wadanda harin ya shafa, sannan ya bukaci duka hukumomin bayar da agajin gaggawa su hanzarta kai daukin gaggawa ga wadanda abun ya shafa
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Lahadi a cocin St Francis Catholic Church, dake Owa-luwa Street, a masarautar Owo Kingdom, dake jihar Ondo inda rahotanni farko ke cewa gomman masu ibada sun mutu