Ba za a tursasa wa kowa dan takara ba kuma bani da kowa a rai a matsayin dan takara ta –inji Buhari
Daga Muryoyi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nesanta kansa dangane da jawabin shugaban APC da yace Ahmad Lawan ne dan takararsa a 2023,
Shugaba Buhari yace babu wanda ya zaba a matsayin dan takararsa a APC na shugaban kasa a zaben 2023 kuma ba zai bari APC ko Gwamnoni ko wani ya tursasa wa kowa dan takara ba.
- Advertisement -
A dazu ne dai aka fitar da rahoton yadda shugaban APC na kasa yace Buhari ya zabi Ahmed Lawan a matsyin dan takararsa.
Sai dai jim kadan da fitar lanarin sai Gwamnonin Jihohin arewacin Najeriya karkashin jam’iyyar APC suka yi watsi da matsayar shugaban jam’iyyar tasu
Muryoyi ta ruwaito Gwamnonin sun ce suna nan a kan bakansu na mika mulki ga kudancin kasar a zaben 2023.
Buhari yace bai da kowa a ransa, a matsayin dan takararsa zai bari Deliget su yanke hukunci a zaben fidda Gwani