Babban gudunmuwar da jama’a zasu iya baiwa dimokuradiyya a Najeriya shine korar APC a 2023 –inji Atiku

Babban gudunmuwar da jama’a zasu iya baiwa dimokuradiyya a Najeriya shine korar APC a 2023 –inji Atiku

 

 

Atiku Abubakar ya ce babbar karramawa da jama’a zasu iya baiwa jaruman dimokuradiyya shine korar Gwamnatin APC a 2023

 

Muryoyi ta ruwaito Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kori jam’iyyar APC daga mulki a babban zabe mai zuwa na 2023.

 

Ya yi wannan kiran ne a yau Lahadi a cikin sakonsa na ranar dimokuradiyya, inda ya ce wannan ita ce babbar karramawar da jama’a za su iya bayarwa ga jaruman dimokradiyya a kasar nan.

 

- Advertisement -

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, a bayyane yake cewa gwamnati mai ci ta kawo wa al’umma mafi muni na gwamnati.

 

Don haka ya roki yan Najeriya su yi watsi da gwamnatin APC wacce ya bayyana a matsayin maras mutunci, wacce ta kawo rashin jin dadi, kunci, da kuma rashin sanin ya kamata.

 

Muryoyi ta ruwaito Atiku ya jaddada cewa duk jam’iyyar da ba za ta iya cika alkawari a kan batun tsaro, bunkasar tattalin arziki, da yaki da cin hanci da rashawa ba, bai kamata a sake zabenta ba domin sake zaben APC tamkar bata wani wa’adi na ‘barna ba’ ne.

 

A cewarsa lallai lokaci ya yi da yan Najeriya zasu tabbatar wa  da ‘yan siyasar APC cewa lallai mulki mallakin jama’a ne ta hanyar amfani da katin zabensu a 2023 su zabi sabuwar Gwamnatin PDP

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: