Bello Turji ya tuba har ma ya saki duka mutanen da yayi garkuwa dasu?

Bello Turji ya tuba har ma ya saki duka mutanen da yayi garkuwa dasu?

Daga Muryoyi

Wani bayani yana nuna cewa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan, da yayi kaurin suna wajen kisa da fashin jama’a, Bello Turji ya ce ya tuba, kuma ma har ya saki dukkan waɗanda ya yi garkuwa da su.

Sai dai ko a makon da ya gabata wani rahoto ya bulla wanda yake nuna cewa an gwabza wani kazamin fada a daji tsakanin Turji da wasu gungun yan bindiga har takai ga bangarorin sunyi asarar mambobinsu.

- Advertisement -

Rahoton ya nuna cewa Turji ne ya kai harin daukar fansa kan gungun yan bindigar inda ya kashe manyansu.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani a hukumance dake tabbatar da wannan dan bindiga ya ajiye makamai, hakanan ba aji Turjin da kansa ya yi magana akai ba.

Sai dai Muryoyi ta ruwaito dama rikakken dan bindigar ya rika bayanai dake nuna yana so ayi Sulhu har takai ga ya rubutawa Gwamnati wata wasika ta neman sulhu.

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: