Buratai ya fadi hanyoyin da za’a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Buratai ya fadi hanyoyin da za’a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Daga Muryoyi

Buratai ya yi wannan jawabin ne a wurin wani taro na rana daya da aka yi a Abuja domin gano hanyoyin magance rashin tsaro a Najeriya.

Tsohon shugaban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai yayi karin haske kan hanyoyin da yake ganin za’a bi domin kawo karshen matsalar tsaro da ta dade tana addabar Najeriya.

- Advertisement -

Majiyar Muryoyi ta ruwaito Buratai a jawabin da ya gabatar a wani wurin taro na rana daya da aka yi a birnin tarayya Abuja domin gano hanyoyin samar da tsaro a Najeriya,

Ya ce dole gwamnati ta aiwatar da wani tsari da kowanne dan kasa zai taka rawa a harkar tsaro, kuma tsarin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga cikin jama’a, kamar shugabannin addini, matasa, malamai, mata, kungiyoyin jama’a, kafafen watsa labarai, jami’an tsaro da tattara bayanan sirri.

Ya kuma ce akwai bukatar a rika wayar da kan jama’a kan rawar da za su taka wurin samar da tsaro a kasar ta hanyar hukumomin kamar Ma’aikatan Wayar Da Kan Jama’a wato NOA, da sauransu,

Buratai ya kuma ce akwai bukatar a farfado da kamfanin kera makamai na DICON don magance kallubalen rashin isasun makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi.

Wannan na da muhimmanci domin cike gibin karancin makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi da sabbin barazana.

Buratai ya kara da cewa garambawul da ake yi wa rundunar yan sandan Najeriya, siyo sabbin na’urorin tattara bayanan sirri da tsare iyakokin Najeriya zai taimaka sosai wurin samar da tsaro

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: