Ahmed Lawan ne dan takarar Buhari a 2023 inji Shugaban APC na kasa
Daga Muryoyi
Sabon rikici mai zafi ya barke a jam’iyya APC bayan da shugaban jam’iyyar na kasa ya kira taro ya gayawa jiga-jigan jam’iyyar APC cewa Kakakin Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ne dan takarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke so ya gajeshi a 2023.
Majiyar Muryoyi ta ruwaito Sanata Abdullahi Adamu yace amma zasu bar duka yan takara su shiga a buga zaben fidda Gwani na jam’iyyar
- Advertisement -
Watakila wannan ne ya fusata mafi yawan yan takarar inda a wani bidiyo aka gansu sun fito a fusace har ma aka ga yadda Gwamnan Kogi Yahya Bello yake kumfar baki ranshi ya baci
Wannan zabi da alamu ba zai yiwu ba domin kuwa Gwamnoni 11 na jam’iyyar APC sun hakikance suna so a mayar da mulki kudu “dan kudu ya gaji Buhari a 2023” sai dai tuni Mista Buhari ya kirasu domin wata ganawa ta gaggawa wanda ake jiran aji me suka tattauna