DA DUMI-DUMI: Jirgin saman “Nigeria Air” zai karbi Lasisin fara Sufuri a yau Litinin –inji FG

Jirgin saman “Nigeria Air” zai karbi Lasisin fara Sufuri a yau Litinin –inji FG

 

Daga Muryoyi

 

Gwamnatin tarayya tace a yau Litinin 6 ga watan Yuni sabon kamfanin jirgin sama na Najeriya wato “Nigeria Air” zai karbi ‘Lasisi na sufuri’ (Air Transport Licence -ATL) daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa wato NCAA,

 

Sanarwar da ma’aikatar sufuri ta fitar ta ce za ayi bikin karban satifiket din ne a hedkiwatar hukumar NCAA dake filin jirgen sama na Murtala Muhammad dake Abuja.

 

 

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Gwamnatin Najeriya ta ce a yanzu lasisi daya kawai ya rage wa “Nigeria Air domin ya soma aiki gadan gadan” lasisin kuwa da yake jira, shine “Air Operator Certificate (AOC)” wato takardar da zai bada cikakken haƙƙin fara jigilar fasinjoji.

 

Nigeria Air Limited ne zai jagoranci kula da sabon jirgin saman na Najeriya wato Nigeria Air

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: