DA DUMI-DUMI: Yahaya Bello ya ce zai sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba

Yahaya Bello ya ce zai sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kogi kuma tsohon dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC ya bayyana cewa nan gaba kadan zai sake kaddamar da takararsa na neman shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa a ranar Laraba bayan ya gana da shugaban kasa a ofishin sa.

- Advertisement -

Governor Bello, who was at the Villa on a ‘thank you’ visit to the President for allowing him to contest in the presidential exercise, said that what he did with the presidential race is test his might, promising that his next attempt will be supersonic.

Muryoyi ta ruwaito Gwamna Bello, yace yaje Villa ne domin yiwa shugaban kasa ‘godiya’ da ya ba shi damar tsayawa takarar shugaban kasa, ya ce abin da ya yi a takarar shugaban kasa ya gwada karfinsa, inda ya yi alkawarin cewa yunkurinsa na gaba zai zama gagarumi.

Gwamnan jihar ta Kogi ya kuma bukaci mabiyansa da su marawa jam’iyya mai mulki a fadin kasar nan baya a zabe mai zuwa, ya kuma yi kira gare su da kada su karaya da rashin nasarar da ya samu a zaben fidda Gwani na jam’iyyar.

Dangane da yiwuwar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, zai dauki musulmi mataimaki kuwa, gwamnan ya bayyana cewa bai kamata addini ko yanki ya zama sanadi ko abun dubawa ko ma’aunin samun mukami a siyasa ba.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: