El-Rufai ya fadi dalilin ficewar Yahaya Bello daga tattaunawar da Buhari yayi da Gwamnonin Arewa

El-Rufai ya fadi dalilin ficewar Yahaya Bello daga tattaunawar da Buhari yayi da Gwamnonin Arewa

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai, yace Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya fice daga taron da kungiyar Gwamnonin APC na Arewa tayi da Buhari domin nuna kin amincewarsa da matakin da takwarorinsa Gwamnoni suka dauka akan wanda zai yiwa APC takara a 2023.

El-Rufai yace Gwamnoni da Shugaba Muhammadu Buhari sun gana a ranar Litinin amma Yahaya Bello ya fusata yayi ficewarsa tare da kauracewa taron,

- Advertisement -

Gwamnan Kadunan ya cigaba da cewa Jam’iyyar APC nada Gwamnoni 14 daga cikin 19 na Arewa, kuma Gwamnoni 12 daga cikin 14 sun amince mulki ya koma kudu a 2023.

Sai dai da alama wannan mataki bai yiwa Yahaya Bello dadi ba duk da cewa ba shi kadai ne Gwamna dan takara a APC ba akwai Gwamna Badaru na Jigawa.

Amma Gwamnan Kogin ya yanke shawarar kauracewa ganawa da Buhari ya fice a dakin taron don nuna fushinsa wanda yin haka yancinsa ne na Dimokuradiyya.

Kazalika shima a nashi jawabin shugaban Kungiyar Gwamnonin APC Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce saboda dorewar zaman lafiya da adalci da baiwa kowa damarsa tasa Gwamnonin suka yanke shawarar a mika mulki kudu a 2023.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: