El-Rufai ya fadi illolin da Kwankwaso da Peter Obi zasu yiwa APC da PDP a zaben 2023

El-Rufai ya fadi illolin da Kwankwaso da Peter Obi zasu yiwa APC da PDP a zaben 2023

Daga Muryoyi

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce a bisa hasashen da sukayi a yanzu da yuwuwar dan takarar jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo wa jam’iyyar APC cikasa a zaben 2023.

Gwamnan ya ce babu shakka Kwankwaso zai raba kuri’un Jihar Kano sai kuma kila Jihar Jigawa da kuma wani sashi na jihar Katsina.

- Advertisement -

Sai dai ita ma jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar zasu fuskanci kalubale domin dan takarar LP (Labour Party) Peter Obi zai kwashe kuri’un PDP a kudu wanda hakan zai kara karya lagon tasirin jam’iyyar

Muryoyi ta ruwaito El-Rufai a hirarsa da Chennels TV a daren yau ya kuma ce babu wani tasiri da sauran yan takarar zasu yi “gwara ma dai Omosure na jam’iyyar AAC watakila ya samu kuri’u dubu 30″

Amma duk ayi a gama dai in sha Allah muna da cikakken yakini dan takarar mu na APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi nasarar lashe zabe a saukake sai ma ya fidda mataimakinsa zaku sha mamaki”

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: