Gwamnati ta kafa sabuwar doka da zai hukunta jaridun intanet da shafukan bogi

Gwamnati ta kafa sabuwar doka da zai hukunta jaridun intanet da shafukan bogi

Daga Muryoyi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kirkiri ‘Ka’idar Aiki’ wani sabon doka da zai rika sanya ido kan kamfanonin dandalin sadarwar zamani da kuma shafukan sadarwar zamani da jaridun yana masu yada bayanai a yanar gizo.

Sabuwar dokar ta hada da cewa, dole ne a saka ido kan kafafen yada labarai dake amfani da intanet ko dandalin sadarwa wajen yada bayanansu, sannan zai zama dole sai jaridun sunyi rajista sun mallaki ofis, haka zalika zasu rika biyan haraji.

- Advertisement -

Bugu da kari za a rika daukar mataki kan jaridu ko daidaikun mutane da sukayi amfani da kafafen sadarwar zamani wajen cin mutuncin wani ko yada bayanan karya ko bayanan da suka sabawa dokar Najeriya na yada labarai. Kenan dai duk shafukan bogi za a goge su,

Sannan dole duk wanda zai rika yada labarai a intranet yabi ka’idar aiki ta yada labarai.

A daya bangaren kuma dokar ta ce dole ne dandalin sadarwa irinsu Meta, Facebook, Twitter, Tiktok, Snapchat da sauransu sai sunyi rajista da Gwamnati sannan sai sun bude ofis a Najeriya sun ajiye jami’in su. Wannan zai bawa Gwamnati damar daukar mataki akansu da zaran sun bari anyi anfani da dandalinsu wajen yada abunda ya sabawa doka.

Sannan haka zai sa su rika biyan duk wasu kudaden haraji da tara kudaden shiga ga Najeriya.

Hukumar NITDA tare da hadin guiwa da NBC da NCC da Ma’aikatar yada labarai ne zasu kula da sabuwar dokar

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: